(ABNA24.com) Har ila yau, mataimakin ministan masana’antun na Iran ya kara da cewa; A Iran ba a karancin man wanke hannu da ake amfani da shi, haka nan dukkanin sauran kayayyakin fada da cutar ta lumfashi.
Sadeki Niaraki ya kara da cewa; Gabanin bullar cutar corona adadin takunkumin da ake kerawa a Iran a kowace rana, bai wuce 200,000, amma yanzu ya rubanya har sau 3000%
Har ila yau mataimakin ministan masana’antun na Iran ta ce; idan za kirga da takunkumin da masu zaman kansu da masu sa-kai suke samarwa to adadin ya dara miliyan 6 da rabi.
342/